Our website uses necessary cookies to enable basic functions and optional cookies to help us to enhance your user experience. Learn more about our cookie policy by clicking "Learn More".
Accept All Only Necessary Cookies
Rihla Conackriyya icon

Rihla Conackriyya


Usmaniyya
1
  • Sep 30, 2016
    Update date
  • Everyone
  • Android 2.0+
    Android OS

About Rihla Conackriyya

Rihla Conackriyya Of Shaykh Ibrahim Niass - Arabic & Hausa Translation

GABATARWA!!!

Conakriyya! Shine sunan da aka fi sanin wannan kasidar da shi, watakila saboda yawan fadin sunan Conakry da akayi a cikinta, Shaikhu (R.A) ya wake yawaicin muhimman abubuwan da suka faru gareshi a cikin tafiyar da yayi ta tsawon kwanaki sittin wadda a cikinsu ya shiga wadansu garuruwa da suke cikin kasashen Senegal Gambia Mali Guinea da Sirre Leone.

Shaikhu (R.A) ya zuba ilimai masu yawa a cikinta kamar yadda ya fadi wasu ni’imomin da Allah Ta’ala yayi masa.

Sau da yawa masoya suna rera wannan kasida saboda muhimmancinta, saboda haka nake son in bayar da tawa gudummawar ta hanyar fassara kalmominta zuwa harshen hausa saboda dangina hausawa masoya suyi amfani da ita.

Abubuwan lura!:

1- Shaikhu (R.A) ya rubuta sunayen yawaicin idan ba muce dukkan garuruwan da ya ambata a cikin wannan kasida ba, kamar yadda ya ga dama, saboda wata hikima wadda bamu santa ba. Kamar:

"دَكَارَ، بَمَكُ، كُنَاكِرِي، كُومْبِيَا، كُرَسَا، فُوتَجَلاَّ"

A maimakon:

"دَاكَارْ، بَامَاكُو، كُونَاكِرِي، غَمْبِيَا، كُورُوسَا، فُوتَاجَالُونْ".

Da sauransu.

2- Kalmomin da suke cikin alama kamar haka “ “, karin bayani ne domin fahimtar da ma’ana, amma ba su cikin lafazin baitin da ake fassarawa.

3- Shaikhu (R.A) yayi wannan tafiya daga daren karhe na watan Zulhijjah na shekarar 1366 bayan hijira, zuwa daren karshe na watan Rajab na shekarar 1367.

Shaikhu (R.A) ya zo birnin Kano Nigeria zuwan farko a watan Rajab a cikin shekara ta 1364 B.H, domin cika alkawarin da suka yi da Sarkin Kano Alhaji Abdullahi bayero (R.A) a madina, a cikin shekara ta 1355 B.H na cewa zai zo garinsa, Mutum uku suka bishi bayan tafiyarsa, sune:

(1) Shaikhu Sani Hasan Kafanga (R.A).

(2) Shaikhu Tijani Usman Zangon bare bari (R.A).

(3) Alhaji Usman Mazadu Mazan kwarai (R.A).

A farko – farkon shekara ta 1366 B.H. wato shekarar da yayi tafiyar da yayi wannan kasidar a darenta na karshe, saboda haka a lokacin da yayi wannnan kasida babu wanda ya san Kaulakha a cikin mutanen Nigeria sai wadannan mutanen guda uku rak.

Yahya Nuhu Sallau (Khalifa)

Sallawi

Juma’a: 6 – Sha’aban – 1434 A.H.

Daidai da: 14 – June – 2013 A.D.

Auchi, jihar Edo.

Show More

Additional APP Information

Latest Version

1

Uploaded by

Reinaldo Gouveia

Requires Android

Android 2.0+

Content Rating

Everyone

What's New in the Latest Version 1

Last updated on Sep 30, 2016

Minor bug fixes and improvements. Install or update to the newest version to check it out!

Show More

Rihla Conackriyya Screenshots

Rihla Conackriyya posterRihla Conackriyya screenshot 1Rihla Conackriyya screenshot 2Rihla Conackriyya screenshot 3

Related Tags

Popular Articles In Last 24 Hours

Subscribe to APKPure
Be the first to get access to the early release, news, and guides of the best Android games and apps.
No thanks
Sign Up
Subscribed Successfully!
You're now subscribed to APKPure.